19 Afirilu 2017 - 17:05
An sake fitowa muzahara a Kaduna

'Yan uwa a garin Kaduna a arewacin Nigeria sun sake fitowa muzaharar kiran a gaggauta sakin jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky bayan wadda suka gabatar da safe wadda jami'an tsaro suka kaiwa hari da harba hayajki mai sa hawaye da kuma harbi da harsasai masu rai

A jiyaTalata ne dai daukakin birane da manyan garuruwa a fadin Nigeria suka fito muzaharar lumana ta kiran a gaggauta sakin jagoran su wanda gwamnatin Nigeria ke tsare da shi sama da shekara guda bayan mummunan hare hare da aka kai masa da almajiransa a watan Disambar shekara ta 2015.

An gabatar da muzaharar a garuruwan da suka hada da Katsina, Kaduna, Bauchi, Sakkwato, Saminaka, Minna, Jalingo, Lafiya, Illela, Mafara, da sauran su.

A dukkanin garuruwan da aka gabatar da wadan nan muzaharori an tashi lafiya in banda garin Kaduna wanda jami'an tsaro suka auka mata da harbi.

Ga wani yanki na yadda muzaharar ta kasance a yau a garin Lafiya:288